Limamin Tehran: HKI Barazana Ce Ga Tsaron Duniya

Wanda ya jagoranci  sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya fara da yin magana akan halin da ake ciki a kasar Syria wanda

Wanda ya jagoranci  sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya fara da yin magana akan halin da ake ciki a kasar Syria wanda ya kira shi da makarkashiya da makirici da ‘Yan sahayoniya da Amurka su ka kitsa, tare da jaddada cewa, gwagwarmaya ba ta yi rauni ba, ta ma kara karfi fiye da baya.

Ayatullah Khatami ya yi ishara da yadda HKI ta mamaye wani yanki na kasar Syria tare da cewa,samarin wannan kasar ce za su ‘yantar da kasarsu.

Limamin na Tehran ya kuma bayyana cewa; Al’ummar Iran da tsarin jamhuriyar musulunci sun yi nasarar dakile makircin makiya, kuma ba za su taba bari wani mahaluki ya cutar da Iran ba,domin zai fuskanci martani mai tsanani.

Limamin na Tehran ya aike da sako ga kungiyar hadin kan kasashen larabawa,  da kuma kasashen larabawa na wannan yankin da su ka hada a Saudiyya, da Masar yana mai cewa,  Bai kamata su yi shiru akan yadda  Isra’ila take rusa muhimman cibiyoyin Syria.

Ayatullah Khatami ya kuma ce, Manufar HKI a fili take, suna son kafa faffadar Isra’ila wacce za ta hade tekun Euphrate da tekun Maliya, don haka za ta isa ga wadannan kasashen.

Ayatullah Khatami ya kuma ce, lokaci bai kure ba da za a kawo karshen laifukan da ‘yan sahayoniyar suke tafkawa da yana cin karo da dokokin kasa da kasa.

Limamin na Tehran ya kara da cewa, idan aka cigaba da yin shiru, to kuwa anan gaba za ta iso kan masu yin shirun.

Ayatullah Khatami ya ce; HKI tana a matsayin barazanar taro ce ga dukkanin duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments