Limamin Tehran: Hadin Kai Ne Sakamakon Imani Da Ayyukan Kwarai Ne

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya ce; Hadin kai a tsakanin al’umma yana a matsayin sakamako ne da Imani da aikin kwarai. Hujjatul-Islami

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya ce; Hadin kai a tsakanin al’umma yana a matsayin sakamako ne da Imani da aikin kwarai.

Hujjatul-Islami Wal Muslimin Sayyid Muhammad Hassan Abu Turabi ya bayyana cewa; Aiki da hankali, da sani, da fahimtar siyasa tare da ruhi mai tsarki su ne ke haifar da hadin kai.

Limamin ya yi Ishara da hadin kan dake a tsakanin mahukunta da ‘yan kasa da kuma  yin tsayin daka, yana mai kara da cewa, ya zama wajibi a karfafa wannan dankon hadin kan,domin hadin kai koyarwar alkur’ani mai girma ce.

Da yake Magana akan kamon dakarun sa-kai na Basij, limanin na Tehran ya yi Ishara da jawabin jagoran juyin musulunci akan matsayin da dakarun suke da shi. Haka nan kuma ya ce; Dakarun sa kai na Basiji suna da kima da daraja da kuma taka gagarumar rawa acikin dakarun kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments