Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, Ayatullah Ahmad Khatami, ya gargadi shugabannin yahudawan sahayoniyya kan illar duk wani keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, yana mai jaddada cewa: Idan aka sake yin wani wauta, to Iran za ta kaddamar da wani mummunan martani da zai mayar da Tel Aviv garin fatalwa.”
A hudubar sallarsa ta Juma’a a a yau, Ayatullah Khatami ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ita ce ta yi nasara a yakin wuce gona da iri da aka shafe kwanaki 12 ana yi, yayin da yahudawan sahayoniyya suka kasance mafiya hasara.
Limamin ya yaba da irin jarumtar da al’ummar Iran suka nuna a yakin da aka yi a baya-bayan nan, inda ya tunatar da shahadar manyan kwamandojin soji da masana kimiyyar nukiliya. Yana mai nanata cewa: Iran ba zata rushe ba, kuma ba za a taba yin nasara kanta ba, da yardan Allah, amma za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka da alfahari duk da irin makircin da ake kullawa kanta.
Ayatullah Khatami ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar da karfinta a lokacin da ta kai hari kan sansanonin Amurka irin su Ain al-Assad da Udeid da makamai masu linzami, inda ta kasance kasa daya tilo tun bayan yakin duniya na biyu da ta kai wa Amurka hari sau biyu.