Libya: An Yi Wa Saiful-Islam Kaddafi Kisan Gilla  A Jiya Talata

Masu taimaka wa dan gidan tsohon shugaban kasar Libya, Mu’ammar Kaddafi, Saiful Islam sun sanar da cewa; wasu mutane 4 ne  da  su ka yi

Masu taimaka wa dan gidan tsohon shugaban kasar Libya, Mu’ammar Kaddafi, Saiful Islam sun sanar da cewa; wasu mutane 4 ne  da  su ka yi shiga ta Kwamando su ka kutsa cikin gidansa a garin Zantan, su ka yi masa kisan gilla.

A wata sanarwa da masu taimakawa Saiful-Islami Kaddafi su ka fitar, wanda kuma Abdullahi Usman Kaddafi ya wallafa a shafinsa na facebook, ya bayyana abinda ya faru da cewa kisan gilla ne irin na yaudara da wasu  matsorata, masu aikata laifi su ka aiwatar.”

Haka nan kuma Usman Kaddafi wanda dan kawun Saiful-Islam ne, kuma daya daga cikin wadanda suke aiki da shi a fagen siyasa ya ci gaba da cewa; Makasan sun yi kokarin share sawun laifin da su ka tafka, ta hanyar kashe na’urorin daukar hoto da suke a zagayen gidan Saiful-Islam, sun kuma yi musayar wuta da shi, kafin a karshe su ci karfinsa, rai ya yi halinsa.”

Shi kuwa lauyan Saiful-Islam, Marcel Desailly ya ce; makasan, zaratan makasa ne , kwamandos, su 4, su ka kutsa cikin gidansa dake garin Zantan.

Haka nan kuma, ya fada wa kamfanin dillacin labarun Faransa cewa, tun kwanaki 10 da su ka wuce, ya ji daga bakin wani makusancin Saiful-Islam cewa; Da akwai matsala akan harkokin ba shi kariya da tsaro.

Shi kuwa tsohon mai Magana da yawun gwamnatin Mu’ammar Kaddafi ya ce; Kisa ne na yaudara, domin shi mutum ne da yake son ganin Libya a matsayin kasa dunkulalliya mai tsaro da zaman lafiya.:

Har ila yau, ya bayyana kisan da cewa,kashe fatan da Libya take da shi ne.

Saiful-Islam dan shekaru 53 yana daya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban kasar ta Libya Mu’ammar Kaddafi, wanda kuma gabacin 2011 ana daukarsa a matsayin wanda zai gaji mahaifin nashi.

Bayan kifar da gwamnatin Kaddafi a 2011, an kama shi,tare da yi masa shari’a a tsakanin 2012 zuwa 2013. A shekarar 2015 aka yanke masa hukuncin kasa, bisa laifin murkushe masu bore, haka nan kuma kotun duniya ta manyan laifuka ta fitar da sammacin kamo shi ta hanun hukumar ‘yan sandan duniya ( Interpol).

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments