Lebanon: Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jaridar Tashoshin Almayadeen Da Almanar

Isra’ial ta kaddamar da hare-haren ne ta sama a kan wadannan ‘yan jarida, inda ta harba makamai masu linzami guda hudu a kan motarsu, lamarin
Lebanon: Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jaridar Tashoshin Almayadeen Da Almanar

Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a kan ‘yan jarida a lokacin da suke gudanar da aikinsua kudancin kasar Lebanon a wannan Asabar, lamarin da ya yi sanadin shahadar ‘yan rahoto na tashoshin Almayadeen da Almanar.

Isra’ial ta kaddamar da hare-haren ne ta sama a kan wadannan ‘yan jarida, inda ta harba makamai masu linzami guda hudu a kan motarsu, lamarin da ya yi sanadin yin shahadar Fatima Futuni ‘yar rahoton tashar Almayadeen, da kuma mai daukar hoto kuma dan uwanta shakiki Muhammad Futuni.

Baya ga haka kuma dan rahoton tashar Almanar Ali Shu’aib da suke tare a lokacin shi ma ya yi shahada a nan take. Kamar yadda wasu masu kai daukin gagagwa biyu suka yi shahada a lokacin da suke kokarin ceton wadannan ‘yan jarida, wadanda su ma jiragen yakin Isra’ila suka kawo musu hari.

Daga bisa rundunar sojin Isra’ila ta bayar da hujjar cewa ta kashe Ali Shu’aib ne saboda yana aiki tare da kafar watsa labarai ta kungiyar Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted