Gwamnatin Lebanon ta shigar da karar Isra’ila a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Shafin yanar gizo na Al-Nashra ya bayar da rahoton cewa, tawagar Lebanon ta din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ta gabatar da koke ga kwamitin sulhu na MDD, inda ta bayyana gagarumar damuwa game da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila ke yi.
Koken na Lebanon ya ce Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau 816 cikin kasa da wata guda.
Koken na Lebanon ya jaddada cewa keta yarjejeniyar da Isra’ila ke yi ta hada da hare-haren da take kaiwa a kauyukan dake kan iyakar Lebanon, da wargaza gidaje, da kuma toshe hanyoyi, wanda koma baya ne ga kokarin da ake na daidaita lamarin da kuma hana ci gaba da tabarbarewar tsaro da halin da ake ciki a yankin.
Haka zalika a cewar sanarwar keta yarjeejniyar cikas ne ga kokarin kasa da kasa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.