Lebanon: Sojojin Mamaya Sun Kai Hare-hare A Yankunan Kudancin Lebanon

Da safiyar yau Asabar sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai jerin hare-haren a yankunan kasar Lebanon mabanbanta da su ka hada "Wadi-Saluq" da "Kafar-Tabinit"
Hayaki a wani harin Isra'ila a kudancin Lebanon

Da safiyar yau Asabar sojojin mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai jerin hare-haren a yankunan kasar Lebanon mabanbanta da su ka hada “Wadi-Saluq” da “Kafar-Tabinit” a Nabatiyyah.

“Yan mamayar sun yi amfani da jiragen yaki da kuma manyan bindigogi wajen kai hare-haren a kudancin Lebanon da kuma Nabatiyyah.

Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren ‘yan mamayar sun had agarin Fuqa da ‘al-mansuri da “Wadi-Zabqin.

Wadannan hare-haren dai suna a karkashin keta tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila din take yi da ya kunshi lalata gonaki da kasa da cikin garuruwan kudancin Lebanon.

Kuma duk da cewa gwamnatin Lebanon ta zauna akan teburin tattaunawa da jami’an Haramtacciyar kasar Isra’ila gaba da gaba,amma duk da haka babu abinda ya sauya na hare-haren da ‘yan sahayoniyar suke kai wa Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted