Mutane da dama sun jikkata sanadiyyar wani hari da jirgin sama maras matuki na “Isra’ila” ya kai akan wata mota a garin Hush sayyid Ali dake Bika a gabashin kasar ta Lebanon.
Bugu da kari a lokaci daya Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kuma kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon a yau Alhamis, wanda ci gaba ne da keta hurumin wannan kasa da kuma keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki.
Jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ilan maras matuki dai ya jefa bom ne akan wata mota da take tafiya akan hanyar garin na Hush Sayyid, a Bika da hakan ya jikkata fararen hula.
Tashar talabijin din Almanar ta Hizbullah ta ce, an sami shahidai biyu sanadiyyar wannan harin.
A can kudancin Lebanon ma da safiyar yau Alhamis wasu jerin jiragen sama maras matuki ne su ka jefa bama-bamai a garin Hula, da hakan ya yi sanadin lalata motoci masu yawa na fararen hula da kuma wata buldoza ta aka rami.
A garin Kafar-kalla kuwa sojojin mamayar sun rusa wani gida dake tsakiyar garin bayan da su ka yi kutse a cikin gairn.
Tun da aka kulla yarjejeniyar tsagaita wutar a tsakanin Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila a ranar 27 ga watan Nuwaba na 2024, HKI ba ta taba dakatar da kai hare-haren ba.
A cikin makwannin bayan nan hare-haren nata a kudancin Lebanon da kuma a yankin Bika sun tsananta, da hakan yake sa ana samun shahidai.