Akalla ma’aikatan kafafen yada labarai uku ne suka rasa rayukansu a wani harin da Isra’ila ta kai kan wani rukunin ‘yan jarida a kudancin Lebanon.
Isra’ila ta kai harin ne a yau Juma’a a kan rukunin ‘yan jarida da suka hada da na cikin gida da na kasashen ketare, inda wasu daga cikin ‘yan jaridar suka rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata.
Kafofin yada labaran Labanon sun bayyana cewa, mutane ukun da aka kashe a harin sun hada da ma’aikatan daukar hoto Ghassan Najjar da injiniya Mohamed Reda na gidan talabijin na al-Mayadeen da kuma Wissam Qassem ma’aikacin daukar hoto na al-Manar.
Hakazalika an jikkata wasu ‘yan jarida da dama a harin, wanda shi ne na farko da aka kai a garin Hasbaya, wanda musulmi da kiristoci ke zaune.
Ministan Yada Labarai na Labanon Ziad Makary ya fada a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin X cewa, “Makiya yahudawan sahyuniya sun dira a kan ‘yan jarida a lokacin da suke barci da dare, inda ‘yan jarida 18 ne a wurin da ke wakiltar cibiyoyin yada labarai daban-daban, da suka hada hard a Sky News da Aljazeera.