Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon

Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce da safiyar yau Alhamis  sojojin mamayar HKI sun ketara iyaka su ka shiga cikin garin Balida dake kudancin kasar.

Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce da safiyar yau Alhamis  sojojin mamayar HKI sun ketara iyaka su ka shiga cikin garin Balida dake kudancin kasar.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta amabci cewa bayan da sojojin mamayar su ka kutsa cikin garin na Balida,sun kuma shiga cikin ginin gwamnati, tare da kashe wani ma’aikaci.

Ita kuwa tashar talabijin din “Almanar’ cewa ta yi mutumin da sojojin na mamaya su ka kashe sunan shi Ibrahim Salamah, kuma ma’aikaci ne na karamar hukumar yankin.

Sojojin ma mamaya sun janye, bayan da su ka yi kisa.

Kutsen na sojojin HKI a cikin kasar Lebanon ci gaba ne da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka yi a shekarar da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments