Lebanon : An Zabi Janar Joseph Aoun A Matsayin Shugaban Kasa

An zabi babban hafsan Sojin Labanon, Joseph Aoun a matsayin shugaban kasar.   Aoun ya samu kuri’u 99 daga cikin 128 na majalisar dokokin kasar

An zabi babban hafsan Sojin Labanon, Joseph Aoun a matsayin shugaban kasar.  

Aoun ya samu kuri’u 99 daga cikin 128 na majalisar dokokin kasar Lebanon, tare da goyon bayan bangarori daban-daban na siyasa ciki har da ‘yan majalisar Hizbullah da abokan hamayyarsu.

Zaben nasa ya kawo karshen rashin shugabanci na tsawon lokaci wanda ya kawo cikas ga sauye-sauye da kuma kara fargabar rugujewar a cikin rikice-rikicen da kasar ke fama da su.

Janar din wanda zai yi bikin cika shekaru 61 a gobe Juma’a, yana kuma samun goyon bayan wasu manyan kasashen ketare irinsu Amurka da Saudiyya.

Janar Aoun, wanda ba shi da wata alaka ta iyali da shugaba mai barin gado Michel Aoun, ya jagoranci wata cibiya tun watan Maris din 2017 da ta yi nasarar kaurace wa rarrabuwar kawuna da siyasa da ke wargaza kasar.

Kafin zaman majalisar dokokin na yau Alhamis, an yi kokarin zaben shugaban kasa har sau 12 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments