Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila

A Labanon akalla mutane uku ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a hare-haren jiragen sama marasa matuka na Isra’ila a kudancin Lebanon,

A Labanon akalla mutane uku ne suka mutu sannan goma sha daya suka jikkata a hare-haren jiragen sama marasa matuka na Isra’ila a kudancin Lebanon, wanda ya sake nuna yadda Isra’ilar ke keta yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka cimma.  

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa na Lebanon (NNA), an kashe ‘yan’uwa biyu lokacin da wani jirgin saman Isra’ila mara matuki ya kai hari kan motarsu kusa da garin Shebaa.

Harin ya faru ne a kan wata hanya da ta hada Ain Ata da Shebaa, a kan gangaren yammacin Dutsen Jabal al-Sheikh, wanda ya sa motar ta kama da wuta, kamar yadda NNA ta ruwaito.

Wani hari na danban ya afka wa wata mota a Barashit, inda ya kashe mutum daya sannan ya raunata wasu hudu, a cewar ma’aikatar lafiya ta Lebanon.

Zaman dar-dar ya ƙaru a cikin ‘yan makonnin nan a kudancin Lebanon, yayin da sojojin Isra’ila ke kai hare-hare kusan kowace rana.

Tun lokacin da suka fara kai hare-haren kan Lebanon a watan Oktoban 2023, sojojin Isra’ila sun kashe sama da ‘yan Lebanon 4,000 tare da raunata kusan 17,000, a cewar majiyoyin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted