Firaministan kasar Labanon Najib Mikati ya yi kira da a tsagaita bude wuta da Isra’ila, a yayin da kuma ya bayyana cewa gwamnatin kasar a shirye ta ke ta tura sojoji a kudancin kasar.
Ya bayyana hakan ne ga ‘yan jarida bayan ganawarsa da shugaban jami’an diflomasiyyar Faransa Jean-Noel Barrot, babban jami’in diflomasiyyar kasashen yammacin duniya na farko da ya kai ziyara birnin Beirut tun bayan tsananta hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kasar Lebanon.
Mafita ita ce kawo karshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa Labanon, da kuma komawa ga kiran da Amurka da Faransa suka yi tare da goyon bayan Tarayyar Turai da kasashen Larabawa da na ketare na ganin an tsagaita bude wuta.
Najib Mikati ya kara da cewa muhimmin abin da ya sa a gaba shi ne aiwatar da kudurin MDD mai lamba 1701, wanda ya kawo karshen yakin da aka yi tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a shekara ta 2006.