Ministan harkokin wajen Rasha ya bayyana goyon bayansa ga kasar Lebanon da take fuskantar wuce gona da irin HKI yana mai cewa, Tel Aviv tana take dokokin kasa da kasa ta hanyar amfani da karfi.
Ministan harkokin wajen na Rasha Sergey Lavrov wanda ya gana da takwaransa na Lebanon ya fada wa manema labaru cewa; Rasha tana gudanar da tattaunawa a kwamitin tsaro na MDD domin bayar da kariya ga kasar Lebanon.
Haka nan kuma ya ce; Alakar dake tsakanin Moscow da Beirut tana karfi don haka Rasha a shirye take ta bayar da kariya ga Lebanon.
Ita dai Haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wutar yaki da gwamnatin Lebanon ta watan Yuni 2026 saboda yadda take ci gaba da kai hare-hare a kudancin kasar.
Tare da cewa da akwai kudurin MDD mail amba 2790 da ya bukaci janyewar sojojin mamayar Haramtacciyar kasar Isra’ila daga Lebanon, sai dai har yanzu tana ci gaba da zama a kudancin kasar da kuma kai hare-hare a kusan kowace rana.