Larijani Ya Tattauna Da Mahukuntan Kasashen Qatar Da Iraki

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr.Ali Larijani ya tattauna ta wayar tarho da Fira ministan kasar Qatar, kuma ministan harkokin wajenta Muhammad

Babban magatakardar majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr.Ali Larijani ya tattauna ta wayar tarho da Fira ministan kasar Qatar, kuma ministan harkokin wajenta Muhammad Bin Abdurrahman al-Thani akan abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar ta fitar ta ce, bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu da kuma sauran batutuwan da suke da muhimmanci a wurinsu.

A gefe daya, Dr. Ali Larijani ya tattauna ta wayar tarho da babban mai bai wa gwamnatin Iraki shawara akan harkokin tsaron kasa.

Al-A’araji ya yi wa Allah godiya akan nasarar da Iran ta samu, ta bayannan, yana mai kara da cewa; makiya ba su san cewa al’ummar Iran za ta hada karfi da karfe wuri daya ba, domin tabbatar da hadin kai a tsakaninsu.

Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iraki da al’ummar Iran suna tafiya ne akan tafarki daya, don haka wannan nasarar da Iran ta samu tamu ce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted