Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya yi watsi da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa al’ummar kasar, yana mai bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan wadanda suka aikata kisan gilla a Iran.
Ali Larijani yana mayar da martani ne ga wani sako da Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta yana kira ga masu zanga-zangar da su “karbe cibiyoyin gwamnati” kuma yana mai cewa “taimako yana kan hanya.”
Ya yi ta bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar sau da yawa kuma ya yi barazanar kai hari kan Iran idan aka kashe abin da ya kira “masu zanga-zangar lumana”.
“Mun ayyana sunayen manyan masu kisan gillar al’ummar Iran: 1- Trump 2- Netanyahu,” in ji Larijani a wani rubutu da ya yi.
Yana magana ne game da harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a watan Yunin 2025 na kwanaki 12, wanda ya kashe ‘yan Iran sama da dubu a fadin kasar tare da lalata kayayyakin more rayuwa na farar hula, sojoji, da kuma cibiyoyin nukiliya.
A ranar Talata, wani babban jami’in ‘yan sanda ya ba da rahoton cewa an tsare akalla ‘yan daba 297 da ke da hannu a lalata kadarorin gwamnati da kadarorin jama’a.