Larijani : Tehran a shirye take ta yi tattaunawa “mai adalci da ma’ana”

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya ce Tehran a shirye take ta yi tattaunawa “mai adalci da ma’ana”, muddin ba’a kawo wasu batutuwa da

Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya ce Tehran a shirye take ta yi tattaunawa “mai adalci da ma’ana”, muddin ba’a kawo wasu batutuwa da basu jibanci shirin nukiliya na kasar ba.

Ali Larijani ya ce Tehran a shirye take don tattaunawa mai adalci ta nukiliya wadda za ta magance damuwar da ake da ita.

Dangane da tattaunawar da Amurka, Ali Larijani ya sake nanata cewa za’a mayar da hankali kan batun nukiliya kawai, in ba haka ba, ba za ta yiwu ba.

Ya kuma fayyace cewa batun makami mai linzami, wanda ke karkashin tsaron kasa, ba shi da wuri a wannan tattaunawar kuma ba za a yi wata tattaunawa kan wannan batu ba.

Larijani ya bayyana cewa Iran ta amince da sa ido na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) a karkashin Yarjejeniyar hana Yaduwar Makamai Nukiliya (NPT).

A wani batun kuma Kafin tafiya zuwa Geneva don zagaye na biyu na tattaunawa, kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmail Baghaei ya bayyana cewa Tehran ba ta ga wani amfani ba wajen tsawaita tattaunawar.

A wata hira ta musamman da IRNA, Baghaei ya ce: “Za mu kasance a wannan zagayen tattaunawa tare da kwararru a fannin siyasa, shari’a, tattalin arziki, da fasaha.

” Matsayinmu koyaushe shi ne za mu kasance a wurin tattaunawar domin girmama ‘yancin Iran na amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, gami da wadatar da makamashin.” inji Esmaeil Baghaei.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted