Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya tarbi Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran a hedikwatar shugaban kasa ta biyu dake

Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya tarbi Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran a hedikwatar shugaban kasa ta biyu dake Ain al-Tineh. Larijani ya tabbatar da cewa bayan ganawar da aka yi tsakanin kasashen Labanon da Iran lamarin ya yi kyau da armashi.

Ya jaddada cewa Iran ba ta da niyyar yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan kasar Labanon, yana mai cewa bai kamata wasu kasashe su ba da umarni ga gwamnatin Lebanonba, musamman kan wasu batutuwa masu sarkakiya wadanda al’ummar Lebanon ne tare da gwamnatinsu kawai za su iya yanke shawarar a kansu.

Larijani ya jaddada cewa Iran ba ta zo da wani shiri a Labanon ba, sai dai Amurkawa sun zo ne da takardarsu da ke neman jefa Kasara  cikin yamutsi.

 Larijani ya jaddada cewa Iran na mutunta duk wani matakin da gwamnati za ta dauka tare da hadin gwiwa da sauran bangarori daban-daban na kasar Lebanon.

Kafin nan Larijani ya gana da shugaba Joseph Aoun a babbar fadar shugaban kasa da ke Baabda.

 A wata sanarwa da fadar shugaban kasar Labanon ta fitar bayan ganawar ta bayyana cewa, Larijani ya sake sabunta gaisuwar shugaban kasar Iran ga shugaba Aoun tare da gayyatarsa zuwa birnin Tehran, inda ya kara da cewa “Larijani ya tabbatar da cewa Iran a shirye take ta taimaka wa kasar Lebanon idan har gwamnatin Lebanon tana bukatar hakan so”, inda Aoun ya sanar da Larijani cewa “sha’awar kasar Lebanon na yin hadin gwiwa da kasar Iran a kan dangantakar da ke tsakaninta da Iran abu ne tabbatace.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted