Shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ya bayyana cewa: Iran ba za ta ja da baya a kan matsayinta dangane da mashigar ruwan Hormuz ba
Shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci ta Iran Ayatollah Sadeq Amoli Larijani, ya jaddada cewa: Al’ummar Iran da dakarun kasar sun tsaya tsayin daka kan mashigar ruwan Hormuz, yana mai jaddada cewa: Ikon mallakar wannan hanyar ruwa na Iran ne. Ya bayyana cewa Iran ba za ta ja da baya a mashigar Hormuz a kowane hali ba, kuma wadanda ke neman ‘yancin tafiya da jirgin ruwa dole ne su bi sharuddan Yarjejeniyar Fahimtar Juna da aka cimma.
A farkon taron Majalisar Fayyace Masalahar Tsarin Musulunci, shugaban Mjalisar Ayatollah Amoli Larijani ya lura cewa: Sama da watanni biyar sun shude tun bayan shahadar marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, yana mai jaddada cewa radadin rashinsa yana nan a zukatan wadanda ke fuskantar rashin adalci da aka tafka wa al’ummar Iran. Tare da bayyana cewa: Girman matsayin da yake da shi a tarihi yana kara bayyana kowace rana, yayin da ya hada ilimi, tsoron Allah, gudun duniya, da hangen nesa, wanda hakan ya sanya shi abin koyi na musamman a zamaninsa. Wannan ya bukaci sake bayyana tsarinsa na ilimi da siyasa ga tsararraki na yanzu da na gaba.
Shugaban Majalisar Fayyace Masalahar Musuluncion ya yi dirar mikiya kan Trump da Netanyahu, yana mai bayyana su a matsayin “masu aikata laifuka a tarihi,” kuma ya tabbatar da cewa: Ikirarinsu na kawo karshen yakin cikin kwanaki ko makonni ya rushe a matsayin karya sakamakon juriyar al’ummar Iran. Ya kuma bayyana cewa ayyukan makiya – ciki har da kisan Jagoran, kisan fararen hula, da lalata kadarorin al’adu – sun kunshi laifukan yaki na kasa da kasa, yana mai gargadinsu cewa rashin adalcinsu zai kawo musu karin hasara ne kawai kuma al’ummar Iran ba za su karye ba.