Shugaban babban bankin kasashen Turai Christine Lagarde Ta bada sanarwan cewa kasashen Turai zasu ci gaba da fama da tsada da tashin farashin kayaki a cikin kasashen kungiyar saboda yakin da Amurka ta dorawa JMI zuwa wani lokaci.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Christine Lagardem tana fadar haka ajiya Lahadi, ta kuma ta kara da cewa tashin farashin kayakin zai karu fiye da yanda aka yi hasashe a baya, matukar an ci gaba da yakin da Amurka ta dorawa JMI.
Christine Lagarde ce bankin tarayyar ta Turai ta kara da cewa kasuwar mai zata ci gaba da takurawa kasashen turai na dama, kuma tuni ta tialstawa bankin kara kudaden riba da kuma hana bunkasar tattalin arzikin kasashen nan gaba. Ta ce sau biyu Kenan, tun bayan fara yakin babban bankin kasashen yake kara kudade riba a basussukan bankin, wanda a halin yanzu ya kaishi zuwa 2.5.