Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baqa’I yayi watsi da ikirarin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio yayi cewa Tehran ta sake barar da marta na Tattaunawa , yace karkatar da gaskiyan tarihi ba zai iya goge yadda Washington ta saba karya yarjejeniyoyin da aka cimma daga tunanin jama’a ba.
Baqa’I ya mayar da martani ne game da tambayar da aka yi masa kan ikirarin Robio da yace iran ta sake barar da damarta na tattaunawa , inda ya bayyana a jiya laraba cewa karkatar da gaskiya mai tarihi ba zai goge yawan karyar yarjeniyoyi da Amurka ta yi ba a idon duniya
Haka zalika yayi ishara game da jerin ayyukan rashin gaskiya da Washington ta yi, ciki har da ficewa daga yarjejeniyar nukiliya da radin kanta a ranar 8 ga watan mayun shekara ta 2018 da kuma yadda ta kawo cikas ga hanyoyin diflomasiya da kai hare haren sojan kan iran a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa , da kuma karya yarjejeniyar fahimta ta Islamabad da iran ta cimma da Amurka a ranar 18 ga watan yuni
Daga karshe baqai ya dora alhaki kan kasar Amurka game da dukkan rashin tsaro da zaman lafiya da ake ciki a yankin, da kuma matsalar tattalin arziki da amurka ta fada da ma duniya baki daya.