Kyamar Isra’ila Ta Kara Kamari A Duniya A Cewar Yahudawa

Kafofin yada labaran Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Jawabin Netanyahu ya bayyana zurfin yadda Isra’ila ta zame saniyar ware a duniya Kafofin yada labaran

Kafofin yada labaran Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Jawabin Netanyahu ya bayyana zurfin yadda Isra’ila ta zame saniyar ware a duniya

Kafofin yada labaran Isra’ila sun soki kalaman Netanyahu a Majalisar Dinkin Duniya marasa amfani, suna nuna ficewar wakilai daban-daban tare da tabbatar da cewa jawabin ya nuna wariyar da Isra’ila ta ke fuskanta a duiniya.

A cewar Arabi21, Kamfanin Dillancin Labaran Mehr ya ruwaito cewa: Kafafen yada labaran Isra’ila galibi suna da mummunan ra’ayi game da jawabin Fira Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya. Jaridar Yediot Aharonot ta harshen Ibrananci ta bayyana jawabin Netanyahu a matsayin mai tsauri, girman kai, kuma ba shi da wani hangen nesa na zahiri, tana jaddada cewa Netanyahu yana magana ne da duniyar da ba za ta iya sauraronsa ba.

A cikin nazarin jawabin da ta yi da sharhin da suka shafi hakan, jaridar ta jaddada kalaman Netanyahu masu kaifi game da ficewar wakilan kasashen duniya.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun kuma nuna ficewar wakilan diflomasiyya da yawa a lokacin da Netanyahu ya hau kan mumbari, suna la’akari da shi a matsayin shaida na zurfin yadda duniya take kyamar haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted