Shugaban mulkin soja a Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya bayyana cewa, shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ” zagin dukkan ‘yan Afirka” ya yi a cikin jawabinsa inda yake cewa kasashen Afrika basu da godiyar Allah.
A cikin jawabin bude taron jakadun Faransa a ranar 6 ga watan Janairu a birnin Paris, Emmanuel Macron ya bayyana cewa “tasirin Faransa bai raguwa a Afirka”, duk da kasashen da suka bukaci ficewar sojojin Faransa bisa la’akari da yanayinsu.
Sannan ya kuma bayyana cewa ba dan faransa ba da tun tuni kasashen Afrika sun fada hannun mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Wadannan kalamman nasa sun haifar da martani da kakkausan lafazi da tir da Allah wadai daga kasashen Afirka da dama, musamman Chadi da Senegal.
Martanin baya bayan nan daga shugaban mulkin sojin Burkina faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, ya soki jawabin Emmanuel Macron, inda ya ce “Ya ci mutuncin duk ‘yan Afirka.
‘’Idan akwai wani wanda bai da godiya to shi ne, kamata ya yi idan ya tashi ko wace safiya ya yi adu’a to ya godewa Afrika, saboda ba dan kakaninmu ba da ba’a samar da Faransa ba.