Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da amincewa da Isra’ila ta yi wa yankin Somaliland a matsayin kasa.
Yawancin kasashe membobin kwamatin sun yi Allah wadai da amincewar yankin Somaliland da ya balle a yankin Afirka, inda kasashe da dama suka nuna damuwa kan cewa matakin zai iya yin tasiri sosai ga yanayin Falasdinawa a Gaza.
An kira taron na gaggawa a ranar Litinin biyo bayan shawarar da Isra’ila ta yanke a makon da ya gabata na zama kasa ta farko kuma daya tilo da ta amince da Jamhuriyar Somaliland a hukumance a matsayin kasa mai cin gashin kanta kuma mai ‘yancin kai.
A lokacin da yake jawabi ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, jakadan Somaliya a MDD, Abu Bakr Dahir Osman, ya bukaci membobin su yi Allah wadai da abinda ya danganta da ”zalunci” na Isra’ila.
Ya jaddada cewa matakin na raba Somalia babban hadari, yayin da kuma cikas ne ga zaman lafiya a fadin yankin Afirka da Red Sea.
M. Osman ya ce wannan matakin wani yunkuri ne na ci gaban shirin Isra’ila na tilasta wa al’ummar Falasdinawa kaura daga Gaza zuwa yankin arewa maso yammacin Somaliya.
“Dole ne a dakatar da wannan a yanzu,” in ji shi.
Da yake magana a madadin kungiyar kasashen Larabawa wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Maged Abdelfattah Abdelaziz, ya ce kungiyar na mai watsi da wannan mataki da aka dauka ba bias ka’ida ba da nufin saukake korar al’ummar Falasdinu, ko kuma amfani da tashoshin jiragen ruwa na arewacin Somaliya don kafa sansanonin soja.”
Dama dai kasashen duniya dama da kungiyoyin kasa da kasa sunyi tir da matakin.