A jiya Alhamis ce kwamitin tsaro na MDD ya karbi sabbin mambobi 5 a kwamitin.
Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta bayyana cewa sabbin kasashen da kwamitin ya karba dai sun hada Panama, Pakistan, Denmark, Girka da kuma Somalia. Wadannan kasashe zasu kasance mambobi a kwamitin tsaron na tsawon shekara guda-biyu, a kuma matsayin wadanda ba su da hakkin (Veto) sannan na wucin gadi.
Kwamitin tsaro na MDD dai yana da mambobi 15 ne, 5 daga cikinsu tabbatattun mambobi ne wadanda kuma suke da hakkin hawa kujeran ‘na ki’ wanda ake kira VETO, kuma sune Amurka, Faransa, Ingila, Rasha da kuma Chaina.
Sauran mambobin kwamitin guda 10 ana zabensu ne daga sauran kasashen duniya a majalisar dinkin duniya, kuma duk kasar da aka zama a cikinsu zata yi shekaru biyu ne kacal a kwamitin na tsawon shekara 2. A halin yanzu dai wadannan kasashen 5 zasu hadu da kasashen Algeria, Guyana, the Republic of Korea, Saliyon, da kuma Slovenia, wadanda zasu kammala wa’adinsa a karshen wannan sabuwar shekara.