Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna halin da ake ciki a Sudan musamman batun jin kai
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zama na bayyane domin tattauna batun tabarbarewar harkokin jin kai a Sudan, inda zaman tattaunawa zai fi mayar da hankali ne kan kalubalen da suka shafi samar da abinci da kuma halin da ake ciki a yankunan da rikicin kasar ya fi kamari. Zaman dai yana zuwa ne a matsayin amsa bukatar da kasashen Birtaniya, Ghana da Slovenia suka gabatar, dangane da munanan matsalolin jin kai da suka biyo bayan yakin da aka kwashe watanni ana yi a kasar.
Daraktan ayyuka a ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya shirya gabatar da wani takaitaccen bayani game da cikas da ke hana kai kayan agaji ga yankunan da abin ya shafa da suka hada da Darfur, Kordofan, tsaunin Nuba da kuma Jihohin Khgartoum da Aljazira.
Hasashen na nuni da cewa taron zai yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna da su tsagaita bude wuta cikin gaggawa tare da saukaka hanyoyin tafiyar da ayyukan jin kai, baya ga yin kira ga masu hannu da shuni da kungiyoyin kasa da kasa da su ba da karin tallafi don biyan bukatun da suke karuwa a kasar.