Kwamitin Sulhu Zai Yi Taron Gaggawa Bayan Harin Iran Kan Isra’ila

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce zai yi taron gaggawa yau Laraba, bayan harin da Iran ta kai kan Isra’ila jiya Talata. Kwamitin

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce zai yi taron gaggawa yau Laraba, bayan harin da Iran ta kai kan Isra’ila jiya Talata.

Kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taro cikin gaggawa a wannan Larabar domin tattaunawa kan yadda rikicin yankin Gabas ta tsakiya ke kara ta’azzara, kamar yadda fadar shugaban kasar Switzerland ta sanar ga manema labarai.

Tunda farko dai rundunar sojin Isra’ila ta ce hare-haren za su haifar da mummunan sakamako.

“Muna da tsari, kuma za mu rama a wuri da kuma lokacin da muka ga ya dace,” in ji sanarwar rundunar sojin Isra’ila.

Amurka ma ta ce tana hadin guiwa da Isra’ila, domin tsara mayar da martani kan Iran.

Dama Amurka ta ce ta taimakawa Isra’ila wajen kakkabo makaman da Iran ta harba kafin isa Tel Aviv.

Ita ma dai Jordan ta sanar da cewa ta kakkabo wasu makamman na Iran.

Kafin hakan dai Iran ta yi gargadi ga Isra’ila akan kada ta kuskura ta yi tunanin mayar da martani, inda Iran ta ce hare-haren martani ne ga hare-haren Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments