Kwamitin Sulhu ya yi Allah-wadai da harin da aka kai kan Qatar

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Alhamis, kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kai a Doha babban birnin kasar Qatar, ba tare da ambaton sunan Isra’ila ba. TY kuma jaddada wajabcin daina kai irin wadannan  hare-hare da kuma nuna cikakken goyon baya ga  ga ‘yancin kasar Qatar.

A nata bangaren, mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kwamitin sulhu bayani kan koken na Qatar, inda ta jaddada cewa, harin na Isra’ila ya bude wani babi ne mai hadari a cikin wannan rikici mai muni.

Mataimakin Sakatare-Janar ta kara da cewa “dole ne dukkan bangarorin su dauki matakin kiyaye yunkurin da ake yi na samo hanyoyin tsagaita bude wuta,” tana mai gargadin cewa “duk wani mataki da zai kawo cikas ga tattaunawar yana raunana duk kwarin gwiwa kan hanyoyin da aka  dogara da su ne don magance rikice-rikice.”

A nasa Wakilin Rasha a kwamitin  sulhun ya ce abin da ya faru a Doha ba wani lamari ne da ya auku ba zato ba tsammani,  illa dai hakan sakamakon kawai na rahin hukunta Isra’ila.

Ya kara da cewa Moscow ta yi kakkausar suka kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar Qatar, yana mai gargadin cewa matakin da Isra’ila ta dauka zai haifar da babbar illa ga tsaro da zaman lafiyar duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments