A wani lokaci yau Litini ne Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taro kan rikicin Isra’ila da Yemen.
Za a gudanar da taron ne a hedkwatar MDD, a cewar rahoton kwamitin sulhun.
Isra’ila ta bukaci taron ne bayan wasu hare-hare data fuskanta daga Yemen a baya baya nan, ciki har da harba makami mai linzami da ya raunata mutane 16 a birnin Tel Aviv-Jaffa a farkon wannan watan.
Kungiyar Ansararullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtsi a Yemen ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra’ila da kuma kan jiragen ruwa na kasuwanci a tekun Bahar Maliya, a wani yunkuri na matsawa gwamnatin Isra’ila lamba kan kawo karshen yakin da take yi a Gaza.
Isra’ila ta mayar da martani da hare-hare a San’a da Hodeidah na Yemen, ciki har da harin da ya kashe akalla mutane tara a farkon wannan watan.