Kwamandan sojojin kasa na kasar Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya bayyana cewa tutar kariya da gwagwarmaya za su ci gaba da kasancewa har zuwa bayyanar Imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanar da shi), kuma jaruma sojoji da dakarun da suka sadaukar da rayuwarsu ba za su taba bari tutar ta fadi ba komai tsauri..
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya habarta cewa: A gefen ziyarar da ya kai wa iyalan shahidan yakin kwanaki 12 a Kermanshah, Birgediya janar Heidari ya bayyana cewa: Shahidai suna da matsayi mai girman gaske kuma suna da rawar da ba ta misaltuwa wajen karfafa tsaro da karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Ya kara da cewa: Tutar tsaro da tsayin daka za su kasance suna dage har zuwa bayyanar ma’abucin zamani Imam Mahdi {Allah ya hanzarta bayyanarsa}, kuma jaruman sojoji da wadanda suka sadaukar da rayukansu ba za su taba yin watsi da ita ba.
Ya kuma jaddada cewa: Shahidai ginshikai ne na alfahari da ‘yanci ga al’ummar Iran, kuma sadaukarwar da suke yi tana wakiltar hakikanin tabbacin dorewar tsaron kasar.