Kwamandan IRGC Ya Gargadi Amurka Dangane Da Hari Kan Kasar A Ranar Qudus Ta Duniya

Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar

Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma  tsawon mita 180. Sannan  

Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka.

Dakarun na IRGC dai sun gudanar atisai a ranar Qudus ta duniya a cikin tekun na farisa tare da jiragen ruwan yaki manya-manya da kanana wadanda suka kai kimani 3000.

Babban kwamandan ya kammala da cewa babu wani jirgin leken asirin Amurka da ya shigo sararin samaniyar kasar Iran kuma ba zamu taba barin haka ya faru ba. Yace zasu kare kasashen daga duk wanda yake son shigarta ba tare da amincewrasu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments