Da yake magana a gaban babban zauren majalisar dinkin duniya Yarima mai jiran gado na kasar Kuwait shaikh sabah khalid al-hamad Al-sabah ya bayyana yanayin da ake ciki a yankin gaza a matsayin babban bala’I, yace alumma faladinu da basu da wani mai basu kariya suna fuskantar wahalhalu mafi muni a tarihi.
Har ila yau ya kara da cewa abin da ke faruwa a Gaza kisan kare dangi ne,da kuma share kabilu, don haka wannan ba zai tafi da yin shiru ba, kana ya yi tir da harin da HKI takai kan kasar Qatar kuma yayi barazanar cewa kai hari kan daya daga cikin mambobin kungiyar hadin kan kasashen larabawa, kamar kai hari ne akan dukkansu baki daya,
Yarima yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa na yi aiki da nauyin da ke wuyanta na dakatar da ci gaba da ketar dokokin kasa da kasa a Gaza, domin abin da Isra’ila ke yi a yankin gaza ya jafa tsaro da zaman lafiyan yankin baki daya cikin garari.