Rahotanni daga Chadi na cewa kura ta fara lafawa a N’Djamena, babban birnin kasar, bayan da jami’an tsaro suka dakile wani hari a fadar gwanatin kasar cikin daren da ya gabata.
Kakakin gwamnatin kasar, Abderaman Koulamallah ya ce sojojin kasar sun kashe mutum 18 daga cikin maharan tare da kama shida dada cikinsu, yayin da soja guda ya rasa ransa.
Tuni aka tsaurara matakan tsaro a harabar fadar gwamnatin ƙasar.
An kai harin ne a unguwar Djambal Bahr da ke birnin N’Djamena inda aka yi artabu tsakanin masu gadin fadar da ‘yan bindigar.
Bata kashin, wanda ya dauki kusan awa daya ana yi, jami’an tsaro ne suka shawo kan lamarin da karfe 9.30 na dare haka kuma an jikkata mutum tara.
Kawo yanzu dai ba a bayyana sunayen maharan ba.