Kungiyoyin Gwagwarmayar Iraki Sun Yi  Gargadin Mayar Da Martani Idan HKI Ta Kai Wa Kasar Hari

‘Yan gwgawarmayar na Iraki sun bayyana cewa, idan har ‘yan sahayoniya su ka aiwatar da barazanar da su ka yi na kai wa Irakin hari,to

‘Yan gwgawarmayar na Iraki sun bayyana cewa, idan har ‘yan sahayoniya su ka aiwatar da barazanar da su ka yi na kai wa Irakin hari,to martanin da za su mayar ba zai takaita akan ‘yan sahayoniyar ba, zai shafi kawayensu.

Bugu da kari, ‘yan gwgawarmayar sun kara da cewa, abinda muke fada gargadi ne wanda a baya mun yi shi, muna kuma sake maimiata shi, domin babu yadda za a yi ‘yan Sahayoniya su kawo wa Bagadaza hari ba tare da taimakon Amurka da kawayenta ba.

A jiya Litinin ne dai  ‘yan gwgawarmayar na Iraki su ka fitar da wannan sanarwar sannan su ka kara da cewa; Ba mu yi mamaki ba idan ‘yan Sahayoniya sun yi barazanar kawo hari, to amma su sani mun dade mauna zaune cikin shiri.

Bugu da kari ‘yan gwgawarmayar na Iraki sun kuma ce; Idan har ba a kawo karshen hare-haren  kisan kiyashin da ake  yi  a Falasdinu da kuma Lebanon ba, to ba za mu daina harba jirage marasa matuki zuwa HKI ba.

Kakakin gamayyar kungiyoyin gwgawarmayar ta Iraki Kazim al-Fardusi, ya kuma ce; Idan har bisa kirdado, ‘yan sahayoniya za su yi irin abinda suke yi a Lebanon da Falasdinu, to abinda za mu fada musu shi ne babu lamunin samun nasara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments