Kungiyar “White Helmets Ta” A Kasar Siriya Ta Rasha Tallafin Da Take Samu Daga USAID

Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da

Kungiyar bada agajin ta gaggauwa ta “white Helmets” na kungiyar Al’kaida, wacce kuma take samun tallafin gwamnatin Amurka ta hukumar USAID ta rasa tallafin da take don gudanar da ayyukanta.

Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya bayyana cewa, kasashen yamma musamman Amurka sun yi amfani da kungiyar ta Al-qaeda a lokacin yakin kasar Syriya a shekara ta 2011 zuwa 2017 don ingiza kasashen yamma kan gwamnatin kasar Siriya na cewa ta yi amfani da makaman guba a kan mutane, don cimmmai manufofinsu a kasar ta Siriya.

A halin yanzu dai shugaban Trump zai dakatar da tallafin da ya ke bawa kungiyar mai yuwa saboda sun cimma manufarko a kasar Siriya ta kifar da gwamnatin Bashar a Al’asad. A kalla mutane kimani 40 daga cikin kungiyar ne suka tabbatar da cewa a lokacin yakin sun kai hare kan sojojin Bashar Al-asad, sannan sun yi amfani da wani yaro dan sheakara 5 Omran don farfaganda kan gwamnaton Bashar Al-Asad, kamar yadda mahaifinsa ya fallasa daga baya.

Kasashen Amurka Burtania da Nethalanda duk sun taimakawa kungiyar da miliyoyin dalar Amurka don gudanar da ayyukansu. Amma a bana shugaba Trump ya yanked alar Amurka miliyon 30 da aka warewa kungiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments