Kungiyar UNRWA Ta ce Gaza Ta Zama Makabartar Yan Jarida Da Ma’aikatan Agaji

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya UNRWA yayi gargadin cewa Gaza ta zama yankin da aka fi kashe yan

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya UNRWA yayi gargadin cewa Gaza ta zama yankin da aka fi kashe yan jarida da ma’aikatan Agaji a duniya inda aka kashe sama da yan jarida 230 a yankin Gaza.

kwamishinan hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya janaral philippe lazzarini yace tare da ma’aikatan Agaji sun biya farashi mai tsada, inda sama da mutane 230 daga cikinsu aka kashe,  gaza ce wurin da aka fi kashe mutane a duniya musamman yan jarida, kamar yadda yake kuma wuri ne na kisan ma’aikatan Agaji.

ya kara da cewa hana yan jarida na kasa da kasa da ma’aikatan agaji shiga yankin Gaza take dokokin kasa da kasa ne a fili, yayi kira da a bada yancin yada labarai, kare yan jarida da kuma janye duk wasu matakai da aka dauka na hana yan jarida gudanar da ayyukansu cikin lumana da zaman lafiya.

tun bayan kaddamar da yaki a gaza aka hana yan jarida na kasa da kasa shiga yankin Gaza cikin yanci, ko a larabar da ta gabata ma’aikatar sadarwa ta yankin Gaza ta bada rahoton adadin yan jarida da aka kashe daga lokacin da isra’ila ta kaddamar da yakin kare dangi zuwa yau sun kai 260.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted