Kwamandan Runduna Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan ya yi ikirarin kafa kwamitoci don binciken kisan kiyashin da aka yi a birnin El Fasher
Kwamandan Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Sudan (RSF), Muhammed Hamdan Dagalo “Hemedti,” ya amince a ranar Laraba cewa: Mayakansa sun aikata “keta haddi” a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan. Ya yi ikirarin cewa: An kafa kwamitocin bincike kuma sun riga sun isa birnin domin fara ayyukansu.
A cikin wani jawabi na bidiyo, Hemedti ya ce, “Ya ga keta haddi da aka yi a El Fasher, kuma daga nan ya sanar da kafa kwamitocin bincike, ba kawai kafa kwamitoci ba, har ma kwamitocin bincike sun riga sun isa birnin na El Fasher domin fara ayyukansu.”
Hemedti ya yi ikirarin cewa: “Kwamitocin bincike na shari’a za su fara bincike nan take da kuma daukar alhakin duk wani soja ko jami’i da ya aikata keta haddi ko laifi ga duk wani mutum da aka kama, kuma za a sanar da sakamakon binciken nan take.”
Ya kuma yi ikirarin cewa: “Yanzu an ba da izinin gudanar da zanga-zangar farar hula a El Fasher gaba daya, kuma ana sake duba batun tsare fararen hula don tabbatar da sakin su duk inda aka tsare su. WaÉ—annan umarni ne da za a aiwatar nan take.”
Hemedti ya bukaci mazauna El Fasher “da su koma gidajensu da matsugunansu duk da cikas da ake samu a yanzu na tashin nakiyoyi da sauran ragowar matsalolin yaki.”