Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Musulmi Su Kawo Karshen Killace Gaza

Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen

Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna.

Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana.

Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji na fikihu da su ka wajabta taimakawa wadanda aka zalunta da kawar da zaluncin da ake yi masa.

Fatawar ta kuma bayyana cewa, kin taimakawa wajen taimakawa alhali da akwai dama, yana daidai da yin tarayyar a cikin laifukan yaki.

A wani gefen, bayanin da ya fito daga kungiyar malaman musulmin ya kuma yi kira ga al’ummu da su fito domin yin zanga-zanga da zaman dirshan a gaban ofisoshin jakadancin kasashen Amurka da turai.

Har ila yau fatawar ta bukaci kasar Masar da ta dauki nauyin da ya rataya a wuyanta na tarihi da addini, ta bude mashigar Rafah, saboda a shigar da kayan abinci da dukkanin bukatun yau da kullum. Har ila yau ta ce, yin shiru akan wannan batun bai dace da ma’abota ilimi da addini.”

Wani bangare na sakon kungiyar ta malaman musulunci ya shafi yin kira ga ma’abota tunani da alkalami da su rika aikewa da sakwanni ta shafukansu domin yin matsyin lamba saboda a kawo karsehn wannan bala’in da yake faruwa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments