Babban sakataren kungiyar malaman kasashen musulmi ta duniya ya jaddada cewa: Wajibi ne al’ummar musulmi su yi amfani da dukkanin abin da suke da shi wajen taimakawa Palasdinawa a Gaza.
Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi ya jaddada cewa: Al’ummar musulmi da na larabawa tare da cibiyoyinsu daban-daban karkashin jagorancin kungiyar hadin kan musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, wajibi ne a dauki matakin ceto Falasdinawa a yakin Gaza.”
Al-Salabi a cikin sanarwar da ya fitar ya bayyana cewa: Duniya ta yi watsi da Gaza kuma manyan kasashen da Amurka ke jagoranta suna yin watsi da batun Falasdinu, domin nuna goyon bayansu ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila wacce suke goyon bayanta da dukkan karfinsu.
Ya kara da cewa: Don haka alhakin ceto Palasdinawa a Gaza ya rataya ne a wuyan kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kungiyar hadin kan Larabawa, da kuma kasashe mambobin kwamitin hadin kan yankin tekun Fasha.
Al-Salabi ya jaddada cewa dole kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta dauki Palastinu a matsayin batu na farko. Ita ma kungiyar kasashen Larabawa dole ne ta kalli lamarin Palastinu a matsayin wani babban batu yake a gabanta.
Ya kara jaddada cewa goyon bayan wadanda ake zalunta na daya daga cikin muhimman lamurra a cikin na addinin Musulunci, sanann ya yi kira da a tsaya tsayin daka wajen kare wadanda ake zalunta da kuma kare hakkinsu ta kowace hanya halastacciya. Ya kara da cewa: Falasdinawa suna wakiltar musulmi ne wajen kare alkibla ta farko da wurare masu tsarki na addinin mulunci da suke cikin falastinu.
Al-Salabi ya kara da cewa: Abin da sojojin mamaya suke yi a zirin Gaza kan Falasdinawa a kan idon kotun duniya da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, ba ya da bukatar wani dalili na daban domin tabbatar da tuhuma a kan Isra’ila wajen aikata laifukan yaki.