Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen yankin tekun Fasha (PGCC) ya yi kira da a dage takunkumin da aka kakaba wa Siriya”.
Kasar Saudiyya ta karbi bakuncin taron ministocin harkokin waje, da manyan jami’an diflomasiyya na shiyya, da wasu kasashen yammacin duniya, don tattauna matakan tallafawa kasar Syria.
Yayin taron na jiya Lahadi, wanda ministan harkokin wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud ya jagoranta, an mayar da hankali ga dagewa Syria takunkumai, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyyan ya rawaito.
A daya bangaren kuma kasashen sun yi Allah wadai da wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawan ke yi wa kasar Siriya tare da yin kira da a janye sojojin yahudawan sahyoniya daga yankunan kasar Siriya.
A yayin bude taron kasashen Larabawa da na kasa da kasa kan Syria a birnin Riyadh, Jassim Al-Budaiwi, babban sakataren kungiyar CCGP, ya bayyana yin Allah wadai da hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai wa Siriya.”
Tun barkewar yakin basasar Syria a shekarar 2011, Amurka, da Birtaniya, da kungiyar tarayyar Turai EU, da wasu karin sassa suka kakabawa Syria takunkumai masu tsanani.
Amma bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad a ranar 8 ga watan Disambar bara, Amurka ta dagewa Syria takunkumai na wa’adin watanni 6, domin bayar da damar gudanar da hada-hada tare da hukumomin gwamnatin kasar mai ci, ta yadda hakan zai bayar da damar samar da agajin jin kai, da harkokin da suka shafi makamashi.