Kungiyar kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da mamayar da Isra’ila ke yi wa yankunan kasar Siriya.
Kungiyar mai mambobi 22 ta ce kasashen Larabawa sun yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudanar da zama kan ayyukan Isra’ila a Syria.
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar da cikakkun bayanai inda ta ce kungiyar hadin kan Larabawa ta gudanar da wani taro a birnin Alkahira domin tsara matsayar kasashen Larabawa daya tak game da mamayar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa wasu yankunan Siriya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da su tilastawa Isra’ila janyewa daga yankin Golan da ta mamaye.
Isra’ila ta fara yunkurin karbe wasu yankunan Siriya ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan da mayakan da ke samun goyon bayan kasashen waje karkashin jagorancin Hay’at Tahrir al-Sham (HTS) suka sanar da hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.