Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi Allah wadai da matakin wuce gona da iri da Isra’ila ke dauka kan yankin Golan na Syria da ta mamaye, na karshe dai shi ne amincewar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra’ila na fadada matsugunan yahudawa a cikin yankin Golan da ta mamaye, tare da yin kira ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ta janye daga yankunan da ta mamaye.
Mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa, Saeed Abu Ali, ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin din nan cewa, wannan mataki na Isra’ila, wani gagarumin cin zarafi ne ga Dokokin kasa da kasa da kudurori na MDD, tare da yin gargadin cewa wannan zai kara zafafa tashin hankali a yankin, tare da nuna cewa “wannan yanayin yana kawo cikas ga yunkurin Syria na samun tsaro da kwanciyar hankali, kuma yana hana duk wata dama da za a iya warware rikicin yankin.”
Abu Ali ya tabbatar da yankin Golan da cewa na Siriya ne, da kuma ‘yancin al’ummar na Siriya na samun cikakken ikon mallakar yankunansu bisa ga kuduri na kasa da kasa, wanda ya tabbatar da cewa duk matakan da Isra’ila take dauka a yankin sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva.
Mataimakin Sakatare-Janar ya yi kira ga al’ummar duniya da su matsa lamba kan “Isra’ila domin dakatar da wadannan ayyuka na gaba-gadi, da kuma mutunta kudurori na kasa da kasa.