Kasashen Larabawa Sun Gudanar Da Taron Gaggawa Kan Rikicin Somalia Da HKI

Kwamitin tsaro na MDD da kuma kungiyar kasashen Larabawa zasu gudanar da tarurruka daban daban a yau da kuma cikin wannan makon don tattauna batun

Kwamitin tsaro na MDD da kuma kungiyar kasashen Larabawa zasu gudanar da tarurruka daban daban a yau da kuma cikin wannan makon don tattauna batun yankin Somaliland wanda yake son ballewa daga kasar Somalia, wanda kuma HKI ta amince da ballewarsa a hukumance.

Tashar talabijan ta Press Tv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau Lahadi ce wakilan kungiyar kasashen larabawa a suka hadu a birnin Al-Kahira na kasar Masar cibiyar Kungiyar sun kuma tattaunawa wannan batun suka yi allawadai da HKI, suka kuma bayyana goyon bayansu ga kasar Somalia.

Kungiyar ta gudanar da wannan taron ne, tare da bukatar gwamnatin kasar Somaliya wacce ta damu kan yadda HKI ta amince da ballewar yankin Somaliland daga kasar, wanda ya sabawa hakkin kasar Somalia na yentaccen kasa.

Amincewar HKI da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cikekken yenci, ya nuna cewa tana son rikita yankin gabacin Afirka da kuma kasashen Larabawa. Kuma akwai yiyuwan HKI tare da Amurka suna son su kori Falasdinawa dake Gaza da karfi zuwa yankin na Somaliland.

Kasashen larabawan sun tattauna wannan batun kuma tuni sun bayyana matsayinsu na rashin amincewa da matsayin da HKI ta dauka na amincewa da kasar Somaliland.  Sannan kwamitin tsaron na MDD zai gudanar da nashi zaman gaggawa kan wannan batun na Somalia a gobe litinin. Kasashen duniya suna ganin HKI tana son rikita yankin gabas ta tsakiya gaba daya tare da amincewa da yankin Somaliland na kasar Somalia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted