Kungiyar kare hakkin dan Adam mai sa ido a Siriya ya bayyana cewa: ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan Siriya 14 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Siriya ta bayyana yadda ‘yan bindiga da suke goyon bayan sabuwar gwamnatin kasar ke cin zarafin mutanen da ake ganin suna da alaka da tsohuwar gwamnatin Bashar Assad a wasu yankunan kasar, don haka kungiyar ta yi kira ga sabbin mahukuntan kasar kan su hanzarta daukan matakan shawo kan matsalar.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Siriya ta bayyana cewa: An kashe mutane 14 daga yammacin Juma’a zuwa yammacin jiya Asabar a yankunan Baniyas, Jableh da kuma yammacin Hama na kasar Siriya.
Kamar yadda kungiyar kare hakkin na dan Adam ta jaddada bukatar dakile makamai tare da killace su a hannun jami’an tsaron kasar kawai, tana mai cewa; Ba killace makamai a hannun jami’an tsaro ba, rayuwar dan kasar ta Siriya za ta kasance cikin hadari.