“Human Right Watch” Ta Yi Kira Da A Saki Tsohon Shugaban Nijar Muammad Bazoum

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta yi kira ga gwamnatin sojan jamhuriyar Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Muhamad Bazum, wanda ake tsare da shi tun lokacin juyin mulkin watan Yuli na 2023.

Kungiyar ta kuma ce, ci gaba da tsare Muhammad Bazum da ake yi ba tare da yi masa shari’a ba, ya sabawa doka da kuma take dokokin kasa da kasa na sharia.

 Bayan juyin mulkin na 2023, shugabannin soja sun yi alkawalin gabatar da Bazum a gaban kotu domin yi masa shari’a bisa zargin cin amanar aksa.

A 2024, kotun musamman da aka kafa ta cirewa tsohon shugaban kasar rigar kariya, da hakan ya zama tamkar share fage domin yi masa sharia,sai dai har yanzu hakna ba ta faru ba.

Lauyoyin da suke bai wa Bazzoum kariya sun nemi taimakon kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada MDD da kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ( ECOWAS).

Dukkanin kungiyoyin na kasa da kasa da kuma na yammacin Afirka sun sha yin kira da a saki Bazzum ba tare da wani sharadi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments