Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon sun kaddamar da hare-haren daukan fansa ta hanyar harba tarin makamai masu linzami kan Upper Galilee da yankin Golan na kasar Siriya da aka mamaye, inda ‘yan gwagwarmayar suka fi mayar da martanin kan hedkwatar runduna ta 210 ta Golan da barikin Nafah da kuma hedkwatar rundunar motoci masu sulke na sashin a barikin Yardun.
Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tunkarar hare-haren domin kakkabo makamai masu linzami na Hizbullah, amma abin ya ci tura, lamarin da ya kai ga barkewar tashin gobara a yankunan da aka kai hare-haren.