Kungiyar Hizbullahi Ta Mayar Da Martani Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Labanon tana mayar da martanin gargadi na farko ga gwamnatin ‘yan mamayar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Labanon tana mayar da martanin gargadi na farko ga gwamnatin ‘yan mamayar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ta fitar da wata sanarwa da ke cewa ta kai wani harin mayar da martani na farko na domin kariya da gargadi kan yankin Ruwaisat al-Alam na haramtacciyar kasar Isra’ila, a matsayin martani ga ci gaba da cin zarafi da gwamnatin mamayar Isra’ila take ke yi a cikin yankin kasar Lebanon wanda ya kai ga shahadar fararen hula.

A jiya Litinin ne sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wasu karin hare-hare kan kasar Lebanon a rana ta shida bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta, kuma sun kai hare-haren ne kan wasu kauyuka da suke kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa: A safiyar jiya ne aka ji wata fashewa mai karfi a garin Khiam da ke gundumar Marjayoun, kuma ya ce sojojin mamaya sun harba harsasai 3 a kusa da garin Khiam, sannan kuma an ji karar harbe-harbe da manyan bindigogi a cikin garin.

Don haka adadin saba yarjejeniyar dakatar da bude wutar da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi ya karu zuwa sau 24 da kuma cin zarafi guda 62 tun bayan fara aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakaninsu da kasar Lebanon a safiyar ranar Larabar da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments