A wata sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a yau Laraba ta yi alhinin shahadar Sayyid Hashim Safiyuddin wanda ta bayyana a matsayin dan’uwa ga Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, kuma jagora babba da ya yi shahada akan tafarkin ‘yanto da Kudus.
Sanarwar ta kuma kunshi cewa; Tana mika sakon ta’azaiyyar Shahidin ga ma’abota jihadi,wanda ya hade da shahidi mafi daukaka da girma, sayyid Hassan Nasrallah.
Har ila yau Hizbullah ta bayyana Sayyid Safiyuddin da cewa shi ne madaukin tutar gwgawarmaya ta Shahidi Sakataren kungiyar ta Hizbullah,kuma amininsa da yake dogaro da shi a cikin tsanani da sauki. Haka nan kuma ya kasance ma’abocin tafiyar da sha’anin al’amurran yau da kullum.
Gabanin shahadarsa, Sayyid Hashim Safiyuddin ya kasance shugaban majalisar jihadi ta Hizbullah.