Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullah Ta Kai Wa Sansanonin Leken Asirin HKI Hari

Tashar telabijin din ‘almanar” ta kasar Lebanon ta bayar da labarin dake cewa; Dakarun kungiyar Hizbullah sun kai hari akan na’urorin leken asirin HKI dake

Tashar telabijin din ‘almanar” ta kasar Lebanon ta bayar da labarin dake cewa; Dakarun kungiyar Hizbullah sun kai hari akan na’urorin leken asirin HKI dake yankin Ruwaisatul-Alam ta hanyar harba makamai masu linzami wanda kuma ya yi barna mai yawa.

Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta sanar da kai wani harin akan sansanin sojojin HKI a gabashin sansanin ‘yan share wuri zauna na “Epin-Manahim” ta hanyar amfani da makamai masu linzami.

Wasu sansanonin ‘yan sahayoniyar da kungiyar ta Hizbullah ta kai wa hare-hare su ne, “al-Rahib’ da “Jabalu-Ada’ir”.

Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata, wato kwana daya bayan farmakin “ Guguwar Aksa”, kungiyar Hizbullah ta fara kai wa sansanonin HKI na soja da leken asiri hare-hare.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments