Search
Close this search box.

Kungiyar Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kungiyar Hizbullah ta yi luguden wuta kan arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin mayar da martani ga harin bam da aka kai a kudancin Lebanon

Kungiyar Hizbullah ta yi luguden wuta kan arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila a matsayin mayar da martani ga harin bam da aka kai a kudancin Lebanon

Gidan rediyon sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya sanar da cewa: An harba makamai masu linzami 90 daga kudancin kasar Lebanon kan yankin arewacin Falasdinu da aka mamaye a safiyar jiya Asabar, wanda ya zo daidai da harin bam da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan kudancin Lebanon da kuma kwarin Biqa’a.

A ci gaba da goyon bayan al’ummar Falastinu da suke tsayin daka a Zirin Gaza da kuma goyon bayan ‘yan gwagwarmaya da jajircewarsu wajen mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin makiya yahudawan sahayoniyya da suke kai wa kan kauyuka da suke kudancin Lebanon da gidajen fararen hula, ‘yan gwagwarmayar Musulunci sun yi luguden bama-bamai kan sabon hedkwatar sashin Galili a Ayelet Hashahar Basaliyat da makamai masu linzami.

Kamar yadda a jiyan ‘yan gwagwarmayar Musulunci suka kai hari kan hedikwatar rundunar sojin yahudawan sahayoniyya ta 210 ta Golan dake sansanin Nafah da rokokin Katyusha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments